An kafa dokar kone gawarwakin mamata a Sri Lanka saboda Covid-19, Musulman kasar suna adawa da dokar.
A rahoton da jaridar Strait Times ta fitar an bayyana cewar dangin Musulmai sun nuna rashin amincewarsu da wannan dabi’ar ta rashin binne gawarwakin ‘yan uwansu.
Wani ma'aikacin lafiya na Sri Lanka ya bayyana cewar dangin Musulmai na son binne gawarwakinsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada don haka gawarwaki 19 ke zaune a dakin ajiye gawarwaki ba tare da kulawa ba har tsawon kwanaki 10.
An buga dokar kona gawarwaki a mutanen da suka mutu sakamakon Covid-19 a Sri Lanka a watan Afrilu a cikin jaridar gwamnatin kasar.
Kungiyoyi Masu Zaman Kansu da 'yan tsiraru sun gabatar da korafinsu ga Kotun Koli tare da korafe-korafe 12 game da kona gawarwakin Musulmai. Duk da haka, Kotun Koli ta yi watsi da ƙarar ba tare da ba da wani dalili ba.
'Yan sandan Sri Lanka sun ba da rahoton cewa an kona gawarwaki 5 a jiya.
A cikin wasikar da suka aika wa Firaministan Sri Lanka, Mahinda Rajapaksa, Ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya a Colombo, Hanaa Singer, sun yi kira ga gwamnatin Sri Lanka da ta sake nazarin irin wannan shawarar game da Covid-19.