Majalisar Kasa ta Faransa ta amince da kudirin dokar hana zirga-zirgar jiragen sama zuwa wurare da ke da nisan tafiya na sa’o’i 2 da rabi da mota.
Kafin kudirin ya fara aiki, dole sai Majalisar Dattawa ta zartar dashi.
Kudirin dokar na da niyyar rage yawan sinadarin carbon da ke cikin kasar da kashi 40 cikin 100 nan da shekarar 2030, don kaiwa matakin da ya ke a shekarun 1990.
Masana na jayayya cewa wannan dokar za ta shafi jiragen sama 5 ne kacal daga cikin jirage 100 na cikin gida a Faransa, don haka sakamakon ba zai yi wani tasiri ba game da sinadarin carbon da jirage ke fitarwa.