Yayin babban taron jam’iyyar Democrats da ke gudana a Chicago shugaba Joe Biden ya gabatar da jawabi mai ratsa zuciya da ban tausayi ko da ya ke Harris ta samu gagarumar tarba daga ƙusoshin jam’iyyar, sai dai babban taron ya gamu da zanga-zangar masu adawa da yadda Amurka ke yin biris da kisan da ake yiwa Falasɗinawa a Gaza.
Bayan kammala jawabinsa ne, cikin ƙwalla Biden ya miƙa fitilar takara ga mataimakiyar tasa Harris a daren Litinin.
Dandazon mahalarta taron sun rika kuwwar faɗin ‘‘Biden we love you’’ wanda ke nuna ƙaunar da magoya bayansa ke mishi.
Biden wanda ya doke Donald Trump a zaɓen Amurka na shekarar 2020, ya shafe mintuna 45 ya na jawabi gaban dandazon magoya bayan na Democrats ciki har da iyalanshi.
Taron wanda zai kai har Alhamis ɗin makon nan gabanin ƙarƙarewa sai bayan kammala shi ne Harris za ta samu cikakken goyon bayan jam’iyyar don samun damar fafatawa da Donald Trump a watan na Nuwamba.
Rashin cancanta da kuma yanayin lafiyarsa ya tilasta Biden janyewa daga takarar bayan tun farko Democrats ta amince da tsayawarsa don yin tazarce, amma bayan muhawarar da Trump ya yi masa kaca-kaca, hakan ya sanya korafe-korafen da suka kai ga janyewar shugaban mai ci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI