A harin da kungiyar ta'addar DEASH ta kai a wani gida dake jihar Diyala a gabashin Iraki ta kashe mutum 6 da kuma raunana wasu 6.
Wani jami'in 'yan sanda dake Diyala mai suna Cafer el Vaili, ya bayyana cewa mambobin kungiyar ta'addar DEASH sun kai hari a wani gada dake kauyen Dara karkashin garin Hanekin.
Vaili ya tabbatar da cewa a harin an kashe mutum shida da kuma raunana wasu shidda.
Jami'an tsaron yankin dai sun kaddamar da farmakin kamo mambobin kungiyar ta DEASH da suka aikata wannan aika-aikan.