Darakta Janar ta WTO ta yi gargadi kan rarraba allurar riga-kafin Corona a duniya

Darakta Janar ta WTO ta yi gargadi kan rarraba allurar riga-kafin Corona a duniya

Darakta Janar ta Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala ta yi gargadi game da nuna bambanci da fifiko wajen rarraba allurar riga-kafin cutar Corona (Covid-19) a duniya.

Okonjo Iweala da a baya ta taba rike shugabancin Kungiyar Riga-Kafi ta Duniya, ta zanta da tashar BBC.

Ta ce "A lokacin da ake yi wa 'yan kasashe masu arziki allurar riga-kafin, bai kamata 'yan kasashe matalauta su zauna suna jira ba."

Okonjo-Iweala ta kuma kara da cewa, a 'yan makonnin da suka gabata wasu kasashen duniya sun hana fitar da alluran riga-kafin da aka samar a kasashensu zuwa waje, wanda wannan zai hana a magance cutar a duniya baki daya.

Ta ce "Idan kowacce kasa ta ce za ta kare kanta kawai daga sabon nau'in cutar, to ba kasar da za ta zauna lafiya."

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ma ya yi kira ga kasashe masu arziki da su taimaka wajen ganin an yi wa 'yan kasashe matalauta allurar riga-kafin.


News Source:   ()