Dangantaka tsakanin ƙarancin bitamin D da mutuwa daga Covid-19

Dangantaka tsakanin ƙarancin bitamin D da mutuwa daga Covid-19

Masana kimiyya da fasaha sun gano cewa akwai wata alaka tsakanin kashe al'umma da coronavirus ke yi da rashin bitamin D a jikin bil adama.

Dangane ga binciken da "Nypost.com" ta yada masana kimiyya da fasaha a jami'ar Northwestern dake Amurka sun yi bincike akan marasa lafiya masu dauke da Covid-19 da ake yiwa jinya a asibitocin Amurka, Jamus, Italiya, Birtaniya, Spain, Swiss, Iran, Koriya ta Kudu da China.

Masanan sun bayyana sun gano cewa a kasashen da Covid-19 ta fi kashe mutane kamar su Italiya, Spain da Birtaniya marasa lafiyan nada karancin bitamin D fiye da na kasashen da aka samu karancin mutuwa daga cutar ta Corona.

Daraktan dakin binciken jami'ar Vadim Backman, ya bayyana cewa duk da cewa an gano akwai alaka tsakanin kashewar da corona ke yi da rashin bitamin D, bai kamata a tilastawa kowa shan bitamin D ba.

Backman, ya kara da cewa akwai bukatar a kara yin kwakkwarar bincike akan lamarin. Ya kara da cewa, 

"Muna fatan bincikenmu zai taimaka akan wannan lamarin. idan aka kara gasganta lamarin zai taimaka wajen warkad da marasa lafiya"

Masu binciken sun kuma yi gargadi game da wuce gona da iri a shan bitamin D din.


News Source:   www.trt.net.tr