An bayyana cewa, mutumin da ya tallawa Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron mari a lokacin da ya ziyarci yankin Drome, Kwararren Dan Kokawar Tarihi ta Turai ne.
Jaridun Faransa sun bayyana cewa, mutumin na da kwarewar wasan takobin Gabas Mai Nisa da ake kira HEMA.
Haka zalika an bayyana cewa, mutumin na bibiyar shafukan sadarwa na zamani na masu tsaurin ra'ayi.
Ofishin gabatar da kara na Valence ya sanar da cewa, mutumin mai shekaru 28 Damien T. da aka kama tare da abokinsa ba su taba aikata wani mugun laifi a baya ba.
A lokacin da dan ta kifen ke marin Macron ya yi irin ihun da ake yi na "Montjoie Saint-Denis" a lokacin da yakin Masarautar Faransa tare da cewa "Tir da Tsarin Macron".
Bayan da Macron ya ziyarci makarantar sakandire ta yawon bude ido a garin Tain-I'Hermitage ne ya je ya yi sallama ga dandazon mutane da ke jiran sa a bayan shingen jami'an tsaro.
A lokacin da ya kusanto wajen ne wani dan ta kife ya sharara masa mari.