Dan ta'adda Brenton Tarrant da ya kai hare-hare a Masallatan Juma'a 2 a garin Christchurch da ke Niyu Zelan tare da kashe mutane 51 da jikkkata wasu 49 ne zai kare kansa da kansa a zaman kotu da za a yi a ranar 24 ga Agusta.
Labaran da Radip Niyuzelan ta fitar na cewar dan ta'addar da ya amsa laifinsa na harin ta'addanci da ya kai Masallatan Juma'a na Nur da Linwood da ke garin Christchurch, ya shaidawa kotu ta hanyar sakon magana daga gidan kurkukun Auckland da yake daure a ciki cewar shi zai kare kansa da kansa a zaman shari'ar da za a yi a nan gaba.
Sakamakon annobar Corona ne ya sanya aka dage zaman kotun da ake sa ran yankewa wa dan ta'addar hukunci, amma a ranar 24 ga Agusta kotun Christchurch za ta zauna.
Ana sa ran yanke hukuncin daurin rai da rai ga dan ta'addar mai cewar farar fata na gaba da kowa a duniya.
A ranar 15 ga watan Maris din 2019 a lokacin Sallar Juma'a, Brenton Tarrant ya kai harin ta'addanci a Masallatai 2 na Nur da Linwood da ke garin Christchurch tare da kashe mutane 51 da suka hada da Baturke 1 da jikkata wasu 49 da suka hada da Turkawa 2.