An bayyana cewa 'yan sanda sun budewa wasu ma'aikatan ma'aiktar wutar lantarki dake kasar Bangladesh dake neman karin albashi wuta lamarin da ya yi sanadiyar rayukan mutum 4.
Kamar yadda The Straits Times ta rawaito, wani jami'in 'yan sandan yankin Chittagong Azizu Islam ma'aikatan dake neman karin albashin sun kaiwa wani dan sanda farmaki lamarin da ya sanya ya bude musu wuta.
Islam ya kara da cewa akallna mutum hudu sun rasa rayukansu kuma da dama, sun raunana, inda ya kara da cewa hankula sun kwanta a halin yanzu.