An bayyana cewar, dan kunar bakin wake mai suna Anthony Quinn Warner dan shekaru 63 ne ya kai hari sa safiyar ranar Kirsimeti a garin Nashville na jihar Tennessee da ke Amurka.
Mai gabatar da kara na Tennessee, Don Cochran ya shaida cewar, sun samu sakamakon da ke nuna dan kunar bakin wake Anthony Quinn Warner ne ya kai harin, kuma ya kashe kansa a wajen sakamakon tashin bam din.
Jami'in Tarayya da ya gudanar da bincike a wajen da aka kai harin ya shaida cewar, gwajin kwayar halitta na DNA da aka yi kan bangarorin jikin dan adam da aka samu a wajen ya nuna Warner ne dan kunar bakin waken.
Mahukunta sun ce, bayan Warner ya ajje motarsa a tsakiyar gari ne ya tayar da bam din da ke daure a jikinsa, sun kuma gamsu cewar shi kadai ya ke gudanar da aiyukansa. Mahukuntan ba su bayyana musabbabin tayar da bam din ba.
An bayyana jikkatar mutane 3 da aka kai asibiti, kuma ba sa cikin mummunan yanayi. A kalla gine-gine 41 ne suka samu matsala sakamakon fashewar, an samu katsewar sadarwar layin 911 da na wayoyin hannu a yankin.