Mutane 5 sun jikkata sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai kan wata cibiyar kula da lafiya da ke jihar Minnesota ta Amurka.
Sanarwar da aka fitar daga ofishin 'yan sandan Buffalo ta ce, wani mai shekaru 67 ne ya kai harin kan cibiyar kula da lafiya.
Mutane 5 sun jikkata, an kuma kama maharin mai suna Gregory Ulrich.
Mahukunta sun bayyana cewa, an gano wasu abubuwa da ake zargi a game da su a dakin otel din da maharin ya ke zaune.