Wani dan bindiga dadi ya budewa al'umma wuta a wata kasuwa dake jihar Calfornia a kasar Amurka lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum biyu.
Dan bindiga dadin ya bude wuta ne inda ya dinga harbin kan mai uwa da wabi a gaban kasuwar Sacramento inda wani dan shekara 19 ya mutu nan take da kuma wani dan shekara 17 ya rigamu gidan gaskiya bayan an kai shi asibiti.
Jawabin da 'yan sandan Sacramento suka fitar sun bayyana cewa an samu cunkoso sanadiyar baje kolin da ake yi na ranar Bakar Juma'a (Black Friday). Haka kuma sanarwar ta kara da cewa kawo yanzu ba'a gano wanda ya kai harin ba.