Ƙasar na ci gaba da matsa ƙaimi wajen ganin an amince mata zama mambar dindindin a kwamitin tsaron da ake son yiwa garambawul na Majalisar Dinkin Duniya.
Wannan yunkuri na kasar na zuwa lokacin da ake tsaka da taron majalisar karo na 79 a birnin New York dake Amurka.
A tattaunawa ta musamman da sashin Hausa na RFI a gefen taron majalisar ɗinkin duniya dake gudana, Ministan harkokin waje na Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya ce ƙasarsa ta fi kowacce ƙarfin tatttalin arziki a Afirka, don haka ta cancanci zama mambar dindindin a kwamaitin tsaro na majalisar.
Ambasada Tuggar ya ce indai dimukuradiyya ake kuma wannan majalisa na wakiltar alummar da suke duniya to tabbas yakamata Najeriya ta riƙe wannan kujera, saboda ita ce ta ɗaya a yawan alumma a Afirka da mutane kimanin miliyan 220.
Ya ce ana kuma ƙiyasta cewa zuwa 2050 ƙasar za ta zama ta 3 mafi yawan alumma a duk duniya.
"Bayan haka Najeriya in ka duba dukda girmanta, da yake tana kewaye da ƙasashen da basu kaita girmaba babu wani yaƙi da ya taba haɗamu da su, muna zaman lafiya da su, muna kiyaye haƙƙinsu”
“Idan ka duba kamar ECOWAS ma in aka samu rashin jituwa ko tarzoma a yankin su, ƙasashen sune suke haɗuwa su da kansu su miƙawa Najeriya ragamar shugabanci” a cewar ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Tuggar
Ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya kuma lissafa ayyuka da dama da Najeriya ta yi waɗanda suka haɗa da tura ƙwararru a fanni daban-daban zuwa ƙasashen Afirka da yankin Caribbean da tsuburi Pacific domin su taimakawa ƙasashen.
Ya ce lura da wannan ayyuka na Najeriya shine ya sa idan aka zo batu na shugabanci ake miƙawa ƙasar domin an san ba za ta tauyewa kowa haƙƙi ba.
Domin kallon bidiyon tattaunawa da ministan harkokin waje na Najeriya Yusuf Tuggar sai ku dannan wannan adireshi: https://youtu.be/rFQTnsymPtw
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI