Dalilan da suka sanya jirage marasa matukan Turkiyya tasiri a fadin duniya

Dalilan da suka sanya jirage marasa matukan Turkiyya tasiri a fadin duniya

Jaridar Die Welt ta Jamus da kuma jaridar Girka sun nanata nasarar da jirage marasa matukan kasar Turkiyya ke cigaba da samu a doron kasa.
Jaridar Die Welt ta mai da hankali ne kan jirage marasa matukan Turkiyya kasancewar irin tasirin da suke ci gaba da samu a fadin duniya.

A cikin labarin, an tunatar da cewa Poland, membar NATO, ta ba da yi yarjejenoiyar siyar jiragen marsa matukan Turkiyya (SIHA) har 24.

Tare da jaddada cewa SIHA ta Turkiyya suna da manyan na’urori, jaridar ta ce, “Turkiyya na maye gurbin Amurka da Isra’ila,” sannan ta jaddada cewa wasu kasashe da dama na son sayen Bayraktar TB2.

Jaridun Girka sun kuma jaddada cewa tare da Bayraktar TB2, Turkiyya ta tabbatar da tasirinta a arewacin Iraki, Siriya da Karabakh, kuma an gudanar da bincike kan cewa Turkiyya ta kara karfi akan harkokin kare iyakokinta .

A gefe guda kuma, wata kafar labarai a Girka,  ta kimanta batun da taken "Me yasa ake sayen SIHA na kasar Turkiyya da dama."

A cikin labarai, an jaddada cewa SIHA na Turkiyya sun sami cikakkun maki a duk inda aka gwada su kuma aka yi amfani da su.


News Source:   ()