An sanar da cewa dalibi mafi tsufa a jami'a a kasar Italiya ya kammala karatunsa na digiri yana da shekara dari ba hudu.
Dalibin jami'a mai suna Giuseppe Paterno wanda ya halarci yakin duniya na biyu mai shekaru 96 ya kammala karatunsa na digiri a sashen tarihi da felsafa a jami'ar Palermo dake kasar Italiya.
An haifi Paterno a shekarar 1923 a garin Sicilya inda ya tashi a cikin iyali marasa hannu da shuni.
Ya kasance wanda ke matukar son litattafai amma bai samu damar shiga jami'a ba. A maimakon haka ya halarci yakin duniya na biyu yana dan shekara 20. Ya dai fara aiki ne a matsayin leburan ma'aikatar hanyar jirgin kasa.
Duk da tsufan da ya yi son yin karatu bai gushe daga zuciyarsa ba, hakan ne ya sanya shi yi kokarin shiga jami'a yana dan shekaru 90.
Wani abin mamaki shi ne duk da kasancewarsa wanda ya girmi ko wane dan ajinsa da kusan shekaru 70; Paterno ya kasance dalibi mafi hazaka wanda ya zo na daya a cikinsu.