An sanar da magance wani dan ta'adda a farmakin kambori-walkiya da ake gudanarwa a arewacin kasar lraki.
Ma'aikatar harkokin tsaron kasar Turkiyya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa ana cigaba da gudanar da farmakin kambori walkiya a Metina da Avashin Basyan dake Arewacin Iraki kamar yadda aka shirya.
Dakarun kasar Turkiyya sun sha alwashin cewa ba zasu bar jinin shahidansu a yankin Avashin Basyan da suke gudanar da farmakin kambori walkiya ba. Akan hakan ne suka yi nasarar magance wani dan ta'addan PKK gabanin ya tsere.