Dakarun sojin Turkiyya da ke Katar na horar da sojojin kasar dabarun harba bama-bamai.
Sanarwar da Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta fitar ta shafinta na Twitter ta ce, dakarun Turkiyya da ke aiki a karkashin Rundunar Hadin Gwiwa ta Turkiyya-Katar, na bayar da horo kan dabarun harba bama-bamai da dakarun Katar. Ana amfani da bam mai girman milimita 120 wajen bayar da horon.