Ma'aikatar Tsaro ta Turkiyya ta bayyana cewar dakarunta na ci gaba da kwance bama-bamai a yankin Karabakh na Azabaijan bayan kubutar da yankin da aka yi daga mamayar Armeniya.
Ma'aikatar ta sanar da cewa, kwararru kan nema da kwance bama-bamai 136 suke gudanar da aiyuka a yankin Karabakh na Azabaijan.
Sanarwar da aka fitar a shafin yanar gizon Ma'aikatar ta ce "A yankin Karabakh da dakarun Azabaijan suka nuna bajinta da sadakarwa wajen kubutarwa daga mamayar Armeniya, ana ci gaba da kwance bama-baman da aka binne."
Sanarwar ta kuma ce, akwai ma'aikatan OMAT masu nema da kwance bama-bamai 136 da ke aiki a Karabakh, kuma suna bayar da horo ga sojojin Azabaijan.