Dakarun Sojojin Turkiyya na bayar da Horon Tsaron Karkashin Ruwa ga Ma'aikatan Sojojin Ruwa na Libiya.
Sanarwar da Ma'aikatar Tsaron Kasa (MSB) ta fitar ta shafukan sada zumunta ta bayyana cewa,
"Muna ci gaba da horar da sojojin Libiya don tallafa wa 'yan uwanmu na Libiya, wadanda muke da dangantaka da ta fuskoki daban-daban har na tsawon shekaru 500 na tarihi."
Sanarwar wacce ta bayyana cewa an ba da horo na Tsaron Karkashin Ruwa ga Ma'aikatan Sojojin Ruwa na Libiya ta kuma hada da hotunan aiyukan horon.