dakarun Taliban sun kashe sojin Pakistan a wata aranagama da suka yi

dakarun Taliban sun kashe sojin Pakistan a wata aranagama da suka yi

Wata majiyar tsaro ce ta Pakistan ta bayyana cewa dakarun Afghanistan sun kashe mata soji guda, tare da jikkata wasu 7 a wata musayar wuta da dakarun ɓangarorin biyu suka gwabza a kan iyakar kasar, yayin da daruruwan 'yan kasar suka yi zanga-zangar nuna adawa da mummunan harin da aka kai musu ta sama wanda ya haddasa rikicin.

Jami'an kasashen biyu sun bayyana cewa, an gwabza kazamin faɗanne a cikin dare, wadda akayi amfani da manyan makamai, tsakanin dakarun da ke kan iyaka tsakanin lardin Khyber Pakhtunkhwa na Pakistan da lardin Khost na kasar Afganistan.

Musayar wutar na zuwa ne bayan da mahukuntan Taliban na Afghanistan suka zargi Pakistan da kashe mutane 46 musamman mata da yara a wani harin da jiragen yakinta suka kai a kusa da kan iyaka a lardin Paktika da ke kudu maso gabashin kasar a cikin makon nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)