An sanar da cewa jami'an tsaron lsra'ila sun kame Falasdinawa 37 da suka hada da wani dan jaridar Falasdin daya a yankin Zirrin Gaza da Gabashin Kudus.
Wata kungiyar Falasdinawa ce ta fitar da sanarwa a rubuce dakarun lsra'ila sun kai farmakin kin kari a yankin Zirrin Gaza da Gabashin Kudus da dare.
Sanarwar ta kara da cewa dakarun lsra'ila sun kame Falasdinawa 20 a Zirrin Gaza da kuma 17 a Gabashin Kudus.
Daga cikin Falasdinawa da aka kama a Zirrin Gaza akwai wani dan jarida mai suna Tarik Abu Zaid.