A yayinda dakarun Libiya ke cigaba da kalubalnatar mayakan Halifa Haftar a kudancin Libiya, sun yi nasarar karbe sansanin sojin Hamza mai muhinmanci.
Mai magana da yawun sojin kasar Kanal Muhammed Kununu, ya sanar da cewa sojojin gwamnatin kasar suin yi nasarar karbe sansanin sojin Hamza daga hannun mayakan Halifa Haftar.
A yayinda Kanunu ke bayyana cewa dakarun kasar na cigaba da kalubalantar mayakan Haftar suna kuma rufe ramukan muguntan da suka gina musu ta kwance abubuwan fashewar da suka dasu musu.
Ta yiwu ganin nasarar da dakarun Libiya ke samu akan mayakan Haftar ne ya sanya mayakan kai hari a kusa da filin tashi da saukar jiragen saman Mitiga dake Tripoli da safiyar sallah.