Dakarun kasar Turkiyya sun horar da sojojin ruwan Libiya har na tsawon makonni biyar akan harkokin samar da tsaro a karkashin teku.
Kamar yadda ma'aiktar harkokin tsaron kasar Turkiyya ta sanar dangane ga Yarjejeniyar Horaswa tsakanin kasashen biyu sojojin kasar Turkiyya sun koyawa na Libiya salon tsaron ruwa iri daban-daban.
Sanarwar ta kara da cewa,
"Dakarun kasar Turkiyya sun fara horar da na Libiya akan samar da tsaro a teku, wanna dai lamari ne da ya dauki makonni biyar ana yi. Haka kuma horarwan samawa jiragen ruwa tsaro da aka fara a ranar 20 ga watan Disamba zai dauki makonni 6 ana yi"