Dakarun kasar Turkiyya suna cigaba da horar da takwarorinsu na Libiya inda a wannan makon sunka koya musu shirin yakin tsallen kwado.
Ma'aikatar harkokin tsaron kasar Turkiyya ce ta sanar da cewa a karkashin yarjejeniyar horaswa dake tsakanin Turkiyya da Libiya dakarun kasar Turkiyya na cigaba da koyawa na Libiya dabarun tsaron kasa iri daban-daban.
An tattabar da cewa dakarun Turkiyya da ke bakin aiki sun ba da horo na "SAS (frogman) ga sojojin Libya a Barikin Sosojin Ruwan dake Homs.