Dakarun Isra'ila sun rushe gidan wani Bafalasdine da suka kama

Dakarun Isra'ila sun rushe gidan wani Bafalasdine da suka kama

Dakarun Isra'ila sun rushe gidan wani Bafalasdine a Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka kama ake tsare da shi a kurkuku.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, sojojin Isra'ila sun kai farmaki a unguwar Turmusaya da ke arewacin Ramallah.

Sojojin Isra'ila sun rushe gidan Muntasir Shelbi mai shekaru 44 da aka daure a gidan kurkukun Yahudawa.

Sojojin na Isra'ila sun harba harsashai da hayaki mai sa hawaye ga jama'ar unguwar da suka taru don mayar musu da martani.

Muntasir Shelbi da yake da shaidar zaman dan kasar Amurka, ana zargin sa da kashe Bayahuei dan kama guri zauna da jikkata wasu Yahudawan 2 a ranar 2 ga Mayu.

A ranar 6 ga Mayu kuma sojojin Isra'ila suka kama Shelbi.


News Source:   ()