Dakarun Isra'ila sun kaiwa sojojin Asad hari a Siriya

Dakarun Isra'ila sun kaiwa sojojin Asad hari a Siriya

Dakarun kasr Isra'il sun kai hari ta sama domin kalubalantar sojojin gwamnatin Bashar Asad a Siriya.

Kamar yadda rundunar sojin ta sanar sabili da harin rokokin da aka kaiwa Isra'ila daga Siriya mu ma yau mun gabatar da hari ta sama akan sojojin gwamnatin Asad dake Siriya.

Sanarwar ta kara da cewa a harin da aka kaiwa Isra'ila alhakin na kan gwamnatin Asad, haka kuma zamu mayar da martani akan dukkanin harin da zai kalubalanci 'yancin Isra'ila.

A gefe guda kuma, gidan talabijin din gwamnatin Asad ta El-Ahbar ta sanar da cewa an ji karar fashewar wasu abubuwa a yankin Hadar dake arewacin garin Kuneytra.

An sanar da cewa wani abu kuma ya fashe a iyakar Siriya da Isra'ila. Fashewar abin ya yi sanadiyar lalacewar gidaje, ababen hawa farar hula a yankin Isra'ila.

 


News Source:   ()