Dakarun kasar Azabaijan na ci gaba da samun galaba akan sojojin kasar Armeniya akan farmakan da suka fara na kubutar da wasu sassan kasarsu daga hannun mamayar kasar Armeniya.
Kamar yadda ma'aikatar tsaron kasar Azabaijan ta sanar dakarun kasarta na ci gaba da samun nasara akan na Armeniya a wasu yankuna da dama.
A yankunan da suka samu nasarar sun kuma lalata kayan yakin kasar Armeniya da suka hada da rokoki biyu, grad BM-21 daya, motan sojoji daya, manyan motoci biyu da kuma tanka daya.