Dakarun gwamnatin Asad a Siriya sun kai hare-hare a Idlib tare da jikkata fararen hula 5.
An bayyana cewa, 3 daga cikin fararen hular da aka jikkata na cikin mawuyacin hali.
Dakarun na gwamnatin Siriya da suka hada da mayakan kasashen waje da Iran ke marawa baya, sun kai harin bam a kauyen Al-Bara da ke kusa da hanyar M4.
An jikkata mutane 5 da suka hada da mata 2 da yaro karami 1.
Da tsakar ranar nan ma dakarun Asad sun kai hare-hare da makaman roka a kauyukan Kafarawid, Sfohin da Kensafra da ke lardin Idlib.