Harin da dakarun gwamantin Bashar Asad suka kai yankin Idlib dake kasar ta Siriya ya yi sanadfiyar raunana mutum 7 wadanda biyu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
Dakarun Bashar Asad da suka hada da 'yan ta'addan dake samun goyon bayan dakarun Iran sun kai farmaki a kauyen Al-Bara da nakiyoyi.
A harin mutuim 7 sun raunana wadanda biyu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
An sanar da cewa dakarun gwamnatin Asad sun rinka harba rokoki ta sama a kauyukan Baynin da Deyirsunbul dake yankin Jebel Zaviye a gundumar Idlib.