Rundunan sojin Armeniya ta bude wuta kan sansanonin sojin Azabaijan dake Nakhchivan.
A cikin sanarwar da Ma'aikatar Tsaro ta Azabaijan ta fitar, an ba da rahoton cewa daga kusa da kauyen Arazdeyen na lardin Vedi na Armeniya, an bude wa sansanonin Azabaijan a yankin Hydarabat na lardin Sederek dake Nakhchivan wuta.
A cikin sanarwar, an lura cewa babu asarar rayuka a tsakanin sojojin Azabaijan, kuma sun mayar da martanin da ya dace zuwa bangaren Armeniya.