A cewar jami'an Amurka, Washington za ta bar sojoji kusan 650 a Afghanistan don samar da tsaro ga jami’an diflomasiyya bayan babbar rundunar sojan Amurka ta kammala janyewa daga kasar, wanda aka shirya za a yi a cikin makonni biyu masu zuwa.
Bugu da kari, wasu karin daruruwan sojojin Amurkawa za su ci gaba da zama a filin jirgin saman Kabul, mai yuwuwa har zuwa watan Satumba, don taimakawa sojojin Turkiyya samar da tsaro, a matsayin wani mataki na wucin gadi har sai an gudanar da aikin tsaro da Turkiyya ke jagoranta.
Tuni dai Turkiya ta nuna cewa ba za ta kara tura dakarunta ba don tsaron filin jirgin saman Kabul.