Kungiyar ta'adda ta Daesh ta dauki alhakin kai harin bam na 3 a Kabul Babban Birnin Afganistan inda mutane da dama suka rasa rayukansu.
Fashewar bama-bamai a karo na 3 a ranar Alhamis din nan ta afku a kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na Hamid Kharzai da ke Kabul. An kwashi wadanda suka jikkata zuwa asibitin yankin.
BBC ta samu bayani daga wani babban jami'in kula da lafiya wanda ya bayyana cewa, a kalla mutane 60 ne suka mutu inda wasu 140 suka jikkata sakamakon harin na ba.
Adadin sojojin Amurka 12 ne suka mutu sakamakon harin bam din.
Amma Ma'aikatar Tsaron Amurka ta bayyana an jikkata sojojinta 15.
A gefe guda kuma, kungiyar ta'adda ta Daesh ta dauki alhakin kai harin.
A rana guda an samu fashear bama-bamai har sau 6 a birnin Kabul.
A sanarwar da Shugaban Amurka Joe Biden ya fitar bayan kai harin ya bayyana cewa,
"Muna tunanin 'yan ta'addar Daesh reshen Horasan ne suka kai harin. Muna so su sani ba za mu manta ba, ba za mu yafe ba, za su dandan kudarsu."