Daesh ta dauki alhakin harin ta'addanci a Bagdad

Daesh ta dauki alhakin harin ta'addanci a Bagdad

Kungiyar ta'adda ta Daesh ta dauki alhakin harin ta'addanci da aka kai a ranar Litinin din da ta gabata a Bagdad Babban Birnin Iraki inda aka kashe mutane 30.

Sanarwar da aka fitar a shafin yanar gizon kungiyar ta ce, Daesh ce ta kai harin kunar bakin wake a wata kasuda da ke Bagdad.

Bayanan farko da aka fitar sun bayyana mutuwar mutane 30 sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a wata kasuwa a birnin Bagdad a lokacin da ta cika masu sayayyar shirin Babbar Sallah.

Firaministan Iraki Mustafa Al-Kazimi ya bayar da umarnin a kama kwamandan yankin da aka kai harin, sannan a kuma fara gudanar da bincike.


News Source:   ()