Wasu shaidu sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Reuters cewar, shugaban sojin ƙasar Janar Waker-Uz-Zaman ya jagoranci wani taro da manyan kwamandodinsa cikin dare inda suka yanke hukuncin kin bude wuta a kan masu zanga zangar.
Rahotan ya ce daga bisani sai Janar ɗin ya je ya shaida wa hambarariyar firaministar cewar ba za su iya aiwatar da dokar tilasta wa mutane zaman gida ba kamar yadda ta bada umarni, abin da ya tabbatar da cewar sojojin ba sa tare da ita.
Wani faifen bidiyo ya nuna yadda fusatattun matasa suka kutsa har cikin fadar firaministar, inda suka yi fashe-fashe tare da kwasar ganimar kayayyaki duk da cewa, sojoji na kallon su amma ba su ce musu uffam ba.
Sojoji na tsaftace fadar firaministar da aka hamɓarar bayan masu zanga-zanga sun yi wa fadar warwaso. REUTERS - Mohammad Ponir HossainHasina ta jagoranci Bangladesh na shekaru 20 daga cikin shekaru 30 da suka gabata a zaɓuka har sau 4 kafin wannan zanga-zangar da ta tilasta mata gudun hijira zuwa India.
Yunus zai jagoranci gwamnatin rikon kwarya a Bangladesh
Mutumin da ya taɓa lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel, Muhammad Yunus ne zai jagoranci gwamnatin rikon ƙwarya ta ƙasar Bangladesh, bayan da firaministar ta arce daga ƙasar sakamakon zanga-zangar da matsan ƙasar suka shirya don adawa da fifikon da ake bai wa wasu ƴan tsiraru wajen bada guraben aiki.
Sabon jagoran gwamnatin rikon kwarya a Bangladesh © EPA-EFE via EuroactivDa safiyar wannan Laraba ce Sakataren Yaɗa Labaran shugaban je ka na yi ka na ƙasar, Mohammed Shahabuddin, Joynal Abedin ya sanar da matakin, wanda aka ɗauka a yayain wani taro da ya ƙunshi manyan hafsoshin sojin ƙasar da kuma waɗanda suka shirya zanga-zangar da ta kifar da gwamnatin Hasina.
Yunus, wanda dadadden abokin hamayyar Hasina ne, zai sauka a ƙasar daga birnin Paris nan ba da jimawa ba, inda ya ke aikin ba da shawara ga kwamitin shirya gasar Olympic.
Da yake magana da kafar yada labarai ta AFP, Yunus, ya ce kafa gwamnatin wucin gadi farkon tafiya ne, burin da ake son cimmawa na shirya tsaftaccen zabe zai tabbata sannu a hankali.
Yunus, ya kara da cewa duk wani mataki da za’a dauka daga yanzu ya nada matukar muhimmanci ga cigaban Kasar mu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI