An sanar da cewa fiye da ‘yan gudun hijira miliyan 2.7 wadanda suke fatan komawa kasashensu sun rasa matsuguni a kasashen waje sanadiyar dokokin yaki da kwayar cutar Covid-19 da aka sanya a kusan ko wace kasa.
Hukumar Kula da “Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta bayyana cewa ya kamata a bayar da dama domin komawar wadanda ke neman komawa kasashensu cikin gaggawa.
Hukumar ta ja hankali da cewa rufe iyakoki da kuma dakatar da kai kawo ya sanya dubban ‘yan gudun hijira rashin matsuguni.