Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya bayyana cewa kwayar cutar coronavirus ta haifar da wata babbar gibi akan huldan dake tsakanin kasashe ta ko wace fanni.
A yayinda yake jawabi a taron da aka gudanar ta yaran gizo da Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Halayyar Dan Adam watau SETA ta shirya Cavusoglu ya yi nuni ga yadda Covid-19 ta tabarbare dangantaka da hulda na sashen shirye-shirye, nazari da jin dadain al’umma dake tsakanin kasashen a doron kasa.
A sabili da haka yayi nuni da cewa ya kamata kasashe sun sake duba da sake fitar da wasu tsaruka da al’adun dangantakarsu da sauran kasashe.