Covid-19: Kasashe mambobin WHO sun bukaci a binciki Hukumar

Covid-19: Kasashe mambobin WHO sun bukaci a binciki Hukumar

Kasashen duniya mambobin Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) sun bukaci da a gudanar da binciken na musamman kan yadda Hukumar ta jagoranci aiyukan yaki da annobar Corona (Covid-19).

A yayin taro ta sadarwar Video da aka gudanar a helkwatar Hukumar da ke Geneva,kasashe 194 mambobin WHO sun tattauna kan yadda ake yaki da cutar a duniya da irin bayanan da ta ke ba wa al'umma.

Kasashen 194 sun amince da a gudanar da bincike na kasa da kasa kan ta yaya cutar ta ke harbuwa daga mutum zuwa mutum.

A jawabin rufe taron da Daraktan Janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi, ya ce "Sama da kowa mu muke son a yi bincike da gano gaskiya."

Tedron ya kuma ce WHO za ta ci gaba da jagorantar yaki da annobar a matakin kasa da kasa.


News Source:   www.trt.net.tr