Covid-19: Isra’ila ta sake saka dokar hana fita waje

Covid-19: Isra’ila ta sake saka dokar hana fita waje

An bayyana cewar kasar Isra’ila ta sake shirin dawo da dokar kulle domin magance yaduwar kwayar cutar Corona da ta kara kamari a kasar a ‘yan kwanakin nan.

Dokar hana fita wajen na makonni uku da ya fara da misalin karfe biyu a ranar Juma’a zai kunshi rufe manyan kasuwanni, guraren wasanni da kuma hana taruka.

Bugu da kari al’umman kasar ba zasu yi tafiyar da ta wuce na kilomita 1 daga gidajensu ba.

Dokar zata kasance har da ranar bikin Yahuwada da suke yawan ziyartar ‘yan uwansu da kuma gudanar da tarukan addu’o’i.

Firaiministan kasar Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa dokar ta zama döle ne domin a hana cikowa a asibitocin kasar.

A halin yanzu dai a kasar Isra’ila akwai fiye da mutum dubu 46,000 dauke da kwayar cutar corona da kuma kusan 557 a sashen kulawar gaggawa a cibiyoyin kiwon lafiyar kasar.


News Source:   ()