Covid-19: Iran ta nemi yin musayar fursunoni da Amurka

Covid-19: Iran ta nemi yin musayar fursunoni da Amurka

Mai magana da yawun gwamnatin Iran Ali Rebii ya bayyana cewa kasarsa na fargaban cewa fursunonin Iran dake gidajen wakafi a Amurka ka iya kamuwa da kwayar cutar Covid-19, a sabili da haka Tahran ta kasance a shirye domin yin musayar fursunoni tsakaninta da Washington.

Dangane ga labaran da suka fito daga Kanfanin Dillancin Labaran Daliban kasar Iran ta (ISNA) Rebil wanda ya yi nuni da yadda cutar Corona ke yaduwa kamar wutar daji a Amurka ya bayyana cewa,

"Muna matukar damuwa da lamarin lafiyar Iraniyawa dake fursuna a kasar Amurka. Muna fatan gwamnatin Washington za ta baiwa kiwon lafiya muhimmanci fiye da siyasa"

Rebil wanda ya yi tuni da cewa Iran ta jima shirye akan yin musayar fursunoni da Amurka ya kara da cewa,

"Ma'aikatar harkokin wajen kasarmu ta nemi yin musayar fursunoni da Amurka ba tare da wata sharadi ba amma har ila yanzu Amurkan bata bayar da wata amsa ba"

 


News Source:   www.trt.net.tr