An sallami Shugaban Kasar Amurka Donald Trump daga asibitin Sojoji na Walter Reed inda ya kwanta don kula da shi sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19).
Tun rana Juma'a 2 ga watan Oktob aka kai Trump asibitin Sojoji na Walter Reed, kuma likitocinsa sun ce zai iya komawa gida a ranar Talatar nan.
Trump ya fito daga asitin da kayan aiki, kuma sanye da takunkumi a bakinsa, ya daga wa 'yan jarida da ke jiran fitowarsa hannu, ya nuna musu alamar ba matsala, komai na tafiya daidai.
An dauki Trump a mota zuwa wajen da jirgin sama mai saukar ungulu samfurin "Marine One" wanda ya dauke shi daga Maryland zuwa Washington DC.
Bayan sallamar Trmp din ya fitar da wani sakon bidiyo inda ya ce
"Kar ku bayar da dama ga cutar ta yi awon gaba da ku, kar ku ji tsoron ta."
A bidiyon da aka dauka bayan Trump ya dawo Fadar White House kuma ya yada shaita shafinsa na Twitter ya bayyana cewar "Na koyi abubuwa da dama game da Corona. Kwai wani abu na tabbas. Kar ku bari cutar ta tafiyar da ku, kar ku ji tsoron ta. Za ku yaki cutar."
Trump ya kuma ce Amurka ce ta ke da maganin cutar Corona mafi inganci a duniya.
Ya ce "A lokacin da na fara zuwa asibiti ba na jin dadi sosai. Amma ga shi kwanaki2 na samu lafiya. Ban taba jin dadin jikina kamar na wannan lokacin ba."
Trump ya kuma yi kira ga jama'a da suka kalli bidiyon da kar su mika kawunansu ga cutar Corona inda ya ce "Za mu kua ga aiyukanmu. A matsayina na shugabanku na wuce gaba. Na san akwai hatsari a hanya amma dole ne na yi hakan. Zan zama a kan gaba tare da yin jagoranci."
Shugaban na Amurka ya ce yana jin karfin jikinsa sosai.
Yadda Trump ya saka takunkumi yayin daukar hoto da cire shi a lokacin da zai shiga fadar White House ya janyo suka daga bangarori daban-daban na Amurka.