Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanov Ghebreyesus ya bayyana cewar "Idan sanyi ya zo za mu fuskanci wahala mai tsanani."
A yayin taron da WHO ta gudanar da helkwatarta da ke birnin geneva na kasar Swizalan, Ghebreyesus ya bayyana cewar a yanzu cutar Corona (Covid-19) ta kai wani mataki mai ban tsoro da sanya fargaba.
Ya ce "A lokacin da rabin duniya ke shiga yanayi na sanyi, muna ganin yadda cutar ke karuwa sosai a Arewacin Amurka da Turai. Mun san cewar idan sanyi ya zo za mu fuskanci wahalhalu da dama."
Ghebreyesus ya kuma bayyana gamsuwarsa kan irin matakan da shugabannin wasu kasashen duniya su ke dauka don hana yaduwar cutar da kuma kyautata tsarin kula da lafiya a kasashen.
Ya ce "Ma'aikatan Jiyya da Likitoci na kara samun kwarewa kan yadda za su kula da mai dauke da cutar Corona. Amma a lokacin da aka cika asibitoci kuma, marasa lafiya da ma'aikatan asibitocin na fuskantar wahalhalu da yawa. A saboda haka muke nuna muhimmanci kan bukatar dukkan hukumomi da masu ruwa da tsaki su tashi tsaye wajen ganin an kubtar da tsarin kula da lafiya daga karyewa a kasashensu."
Darakta Janar na WHO akwai bukatar gudanar da kwakkwaran bincike a kasashen da cutar ke kara yaduwa sosai, a killace wadanda suka kamu da wadanda suka yi mu'amala da su, a kuma samar da asibitoci masu kyau sannan a kyautatawa ma'aikatan lafiya.