An sanar da soke taron kolin Majalisar Dinkin Duniya fa za'a gudanar a New York bayan an samu wakilan kasar Nijer biyar dauke da kwayar cutar Covid-19.
Shugaban zauren MDD ta 75 Volkan Bozkır ne ya sanar da cewa samun wakilan kasar Nijer biyar dauke da kwayar cutar Corona ya sanya dakatar da taron kolin mambobin Majalisar mai kasashe 193.
Kasancewar yadda birnin New York ya zama cibiyar cutar Corona ya sanya gudanar da dukkanin taruka ta yanar gizo. An dai bayyana cewa idan yawan wadanda ke kamuwa da cutar Corona suka ragu za'a fara tarukan na ido da ido.