Hukumar kididdigar Tarayyar Turai ta bayyana cewa harkokin yawon bude ido a nahiyar ya ragu da kaso 75 cikin dari a watan Yuni idan aka kwatanta dana bara.
Haka kuma hada-hadar ayyukan nahiyar ya ragu da kaso 16.4 cikin dari a kasashen nahiyar mai mabobi 27 sanadiyar kwayar cutar Covid-19.
Fannonin sufuri sun ragu zuwa kasa da kaso -83.6 cikin dari sai kuma fannin jiragen sama da ya samu raguwa kasa da kaso -73.8, lamurkan masauki da -73.8 sai kuma ma’aikatun siyar da abinci da -66/4 cikin dari.
An dai samu dan bunkasa da farfadowa a watan Yuni fiye da na watan Afirilu a lokacin da aka fara bude harkokin tattalin arziki.
Bulluwar kwayar cutar Corona a China wacce ta yadu a doron kasa ta yi sanadiyar tabarbarewar tattalin arzikin fannoni da dama da suka hada dana yawon bude ido, sufuri, kere-kere da makamantansu a doron kasa.