A awanni 24 da suka gabata mutane 194 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona a Spaniya, wanda shi ne adadi mafi yawa a lokacin zafi.
Alkaluman da Ma'aikatar Lafiya ta Spaniya ta fitar sun nuna cewa, a awanni 24 da suka gabata an samu karuwar mutuwar mutane 194 wanda ya kawo adadin wadanda cutar Corona ta kashe zuwa dubu 80,340 a kasar, adadin wadanda cutar ta kama kuma ya karu da mutane dubu 7,767 wanda ya kama miliyan 4 da dubu 855 da 65.
Duk da akwai raguwar kwanciya a asibiti da kamuwa da cutar a Spaniya, amma kuma adadin wadanda suke rasa rayukansu na daduwa.
Kaso 69,5 na jama'ar Spaniya sun karbi allurar riga-kafin Corona.
Ministar Lafiya ta Spaniya Carolina Darias ta yi bayani a majalisar dokoki cewa, kaso 88 na kamuwa da cutar nau'in Delta ne.