Bayanan da aka fitar sun bayyana cewar Mataimakin Shugaban Kasar Amurka Mike Pence ya kebe kansa a gida sakamakon samun Sakatariyar Yada Labaran ofishinsa Katie Miller dauke da cutar Corona (Covid-19).
Jaridar Bloomeberg ta shaida cewa bayan da a ranar Juma'a aka samu Miller dauke da cutar Corona ne, sai Mike Pence ya dauki matakin kariya na kebe kai a waje guda.
An bayyana cewar gwajin da aka yi wa Pence ya nuna ba ya dauke da cutar amma duk da haka zai kebe kansa don gujewa abun da ka iya zuwa ya komo inda a yanzu zai dinga yin aiki daga gida.
Babu wata sanarwa a hukumance da aka fitar daga Fadar White House game da batun kebe kai da Pence ya yi.
A ranar Alhamis an samu daya daga cikin masu tsaron Trump dauke da Corona, ranar Juma'a kuma aka samu kakakin Mike Pence dauke da cutar, sannan daga baya an samu mai taimakawa 'yar gidan Trump da ke ba shi shawara Ivanka Trump tare da wasu jami'an tsaron leken asiri 11 dauke da covid-19.