Gwamnatin Jamus ta kara wa'adin umarnin da ta ba wa jama'ar kasar na nisantar juna da nisan mita 1,5 zuwa ranar 29 ga Yuni wanda a baya aka bayar da shi zuwa 5 ga watan.
A taron manema labarai da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gudanar ta bayyana cewar har yanzu ba a samu maganin cutar Corona ba, kuma cutar nan nan tare da al'umma.
Merkel ta bayar da misali da yadda mutane da dama suka kamu da cutar Corona sakamakon halartar zaman Coci a watan da ya gabata a jihar Frankfurt.
Ta ce "Muna ganin yadda cutar ta ke yaduwa sakamakon wasu al'amura. Saboda haka dole ne mu kula sosai."
A gefe guda kuma sakamakon yarjejeniyar da gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi suka yi a Jamus an kara wa'adin nisantar juna da nisan mita 1,5 zuwa ranar 29 ga watan Yuni.