Corona da Kungiyar Ta’addar PKK

Corona da Kungiyar Ta’addar PKK

Kungiyoyin ta’addanci na amfani da gibar da annobar Corona ta haifar. A yayinda duniya ta fada cikin matsalar fama da Covid-19 kungiyoyin ta’addanci ke kokarin amfani da damar. Kungiyar ta’addar DEASH ta kara yawan hare-haren da take kaiwa a cikin ‘yan watannin da suka gabata. Duk da dai daga shekarar 2019 kawo yanzu DEASH na daukar wasu sabbin tsaruka; za’a iya ganin cewa corona ta kasance wata dama dake saukaka kai hare-harenta. Bayan DEASH ma anga yadda kungiyar ta’addar PKK ta kara yawan hare-haren da take kaiwa a kasashen Siriya da Turkiyya. A makon jiya a yankin Afrin din Siriya da ma a Turkiyya PKK ta kalubalanci farar hula. Haka kuma ta kalualnaci taron farar hula a lokacin da ake rabawa al’umma kayan taimako sabili da corona a garin Van din kasar Turkiyya. Hakan dai na nuni da cewa kungiyar ta’addar PKK na amfani da damar matslar da corona ta haifar wajen kara kaimin ta’asar da take aikatawa.

 

Akan wannan maudu’in mun kasance tare da DKt.  Murat Yeşiltaş Daraktan Harkokin Tsaro a Gidauniyar Nazarin Harkokin Siyasa, Tattalin Arziki da Halllayar dan Adam watau SETA…

 

Kungiyar ta’addar PKK na daukar matakai biyu masu karfi don cimma burinsu. Mataki na farkon da suke dauka shi ne yada farfaganda game da annobar  corona a Nahiyar Turai. Ta hanyar bangarorinsu dake Turai suna kokarin yada farfaganda karkashin abinda suka kira Kalubalantar Corona a Turai. Suna amfani da kafafen sadar da zumunta gurin yada bayanan da zai taba tsofi, marasa lafiya da kuma wadanda aka kebe. PKK na tattarawa kansu kudade da sunan yaki da kwayar cutar corona a nahiyar. Wannan shirin na karkashin jagorancin barayin PKK ta mata a nahiyar mai suna (TJK-E) da kuma kungiyar dake wakiltar STK a haniyar watau (KCDK-E). Cibiyar wannan kanfen dai na babban birnin Jamus, Berlin. Kungiyar PKK domin tattarawa kanta kudade da sunan corona ta kafa wani teburin neman agajin gaggawa.

Tsarin PKK na biyu kuwa shi ne kai hare-hare kai tsaye. Daga watan Janairun shekarar 2020 kawo yanzu ta kai hare-hare har guda 9. Biyar daga cikinsu a Turkiyya suka kaisu bayan ranar 10 ga watan Maris da aka fara yaki da kwayar cutar corona a kasar. A watan Afirilu sun kai hari a kauyukan Diyarbaki inda mutum biyar suka rasa rayukansu. A wajen Turkiyya kuma sun kai hare-hare a Arewacin Iraki inda sojojin Turkiyya suke. A ranar 25 ga watan Maris sunkai harin da ya yi sanadiyar shahadar sojojin Turkiyya biyu a ranar 24 ga watan Afirilu kuwa soja daya ya yi shahada a wani harin da suka kai. A dukkan wadanan hare-hare a kauyuka suka kaisu abinda ke nuna cewa basu samu damar kai hari a birane ba. Hakan dai ya faru ne kasancewar yadda sojan kasar Turkiyya suka mayar da himma a karkara inda ‘yan ta’addar ke samun damar yi musu kofar raggo.

Domin kalubalantar hakar dakarun kasar Turkiyya na ci gaba da kalubalantar PKK. Hukumar leken asirin kasar Turkiyya ta MIT da hadin gwiwar rundunar sojin kasar sun gudanar da atasaye 221 tsakanin Janairu-Mayun 2020 a kudancin Turkiyya da arewacin Iraki, a watan Janairu atasaye 44, a watan Febrairu 52, Maris 54 da Afirilu 71. A hare-haren an yi nasarar karbe na’urorin sadarwar kungiyar dubu 17 da 502 da wasu makamai 162. Hukumar ‘yan sanda da hadin gwiwar Jandarma na ci gaba da gudanar da kai farmaki mai taken “bida-gano-lalata” a cikin fadin kasar. Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta bayyana cewa a watan Janairu an kai faramakai dubu 7 da dari 998, a watan Febrariru dubu 5 da dari 584. Haka kuma a farmakan kauyuka 1,385 a watan Maris dubu 7 da dari 119 da kuma a farmakin gururuwa a watan Afirilu an kai dubu 8 da dari 163 a hare-haren 252 an yi nasarar magance ‘yan ta’addar PKK 34.

Duk da dai a ‘yan kwanakin nan an karyawa kungiyar PKK kashin baya, ya kamata Turkiyya ta kara kokarin fitar da wasu sabbin tsarukan kalubalantar ta’addanci. Yanzu dai ba’a za’a iya bayyana cewa ko damar da tsarukan da kungiyar ta dauak ya amfaneta ba. Bayan barkewar annobar corona ana ganin cewa kungiyar ta’addar PKK ta yi amfani da wannan damar inda suka koma kauyuka da kuma amfani da yanayi mai kyau a wannan lokacin. Sai dai  koyaya, bayan Corona a cikin yanayin da ake ciki na siyasar yankin, halin da ake ciki a yanzu a Iraki da rikice-rikicen da ke ci gaba a Siriya, PKK ba za su iya cimma manufar da suke bukata ba.

Wannan sharhin Dkt.  Murat Yeşiltaş ne Daraktan Harkokin Tsaro a Gidauniyar Nazarin Harkokin Siyasa, Tattalin Arziki da Halllayar dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya…


News Source:   www.trt.net.tr