Sakamakon annobar Corona (Covid-19), kungiyoyin Falasdinawa da ke Zirin Gaza sun bukaci da a samar da kariya ta kasa da kasa ga Falasdinawa da ke tsare a gidajen kurkukun Isra'ila.
Rubutacciyar da Gamayyar Kungiyoyin Falasdinawa ta Matasan Musulunci na Kasa Masu Sanya Idanu Kan Fursunoni ta isaga ofisoshin Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, red Cross da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
A wasikar da Kungiyar ta aika wa Hukumomin an bayyana cewar ba a samar da isassun magunguna da kayan kariya, kuma ana ci gaba da kai hare-hare kan FalasdinawaFursunoni.
Wasikar ta ce "Isra'ila na saka sojojinta da ke dauke da cutar su shiga kurkuku tare da yin mu'amala da Fursunoni Falasdinawa da ake tsare da su."
Wasikar ta kuma tabo batun wani Bafalasdine Nacib Abu Va'ar da ya mutu saboda kin yi masa maganin cutar Corona da ta kama shi, a saboda haka aka bukaci kasa da kasa da su taimaka wajen samar da kariya ga Falasdinawa fursunoni.
Akwai Falasdinawa kusan dubu 5 da suka hada da mata da yara kanana a gidajen kurkukun Isra'ila.