Ministan Kiwon Lafiyan kasar Colombia, Fernando Ruiz Gomez, ya bayyana cewa tasirin alurar rigakafin Sinovac na kasar China yana da yawa musanman yadda aka samu raguwar mace-mace a yan shekara 80.
Ruiz, wanda ya tabbatar da nisantar juna a taron ya kara da cewa,
"Akwai tasiri sosai a allurar rigakafin da ake yi a halin yanzu "
Adadin wadanda suka kamu da cutar Korona ya zarce miliyan 3 da dubu 997, kuma adadin wadanda suka murmure ya wuce miliyan 3 da dubu 714 a kasar.
Bogota babban birnin kasar da Antioquia ne aka samun yawan wadanda suka kamu da annobar a kasar.
A halin yanzu mutum dubu 168,800 ke dauke da kwayar cutar Korona a kasar, mafi yawancin wadanda ke sashen kulawar gaggawa daga cikin wadanda ke dauke da cutar yan tsakanin shekara 85-90 ne.