Dangane ga alkaluman da Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ta fitar a ‘yan kwanakin nan an bayyana cewa ciwon dajin mama ya wuce na huhu a matsayin mafi yawan nau’in kansa inda ya kai kusan kaso 12 cikin dari.
Kwararre a fannin ciwon daji a WHO Andre IIbawi ya bayyana cewa a halin yanzu ciwon dajin mama ya zama ciwon daji mafi yawa a duniya.
Ciwon dajin huhu dai ya kasance mafi yawa har na tsawon karni biyu amma a halin yanzu ciwon dajin mama ya tsereshi inda ya kasance na biyu sai kuma ciwon dajin dubura ke binsa a baya a matsayin na uku.
An bayyana cewa an samu karin kamuwa da ciwon dajin mama har miliyan 2.3 a shekarar bara wanda ke nuna kaso 11.7 cikin dari na dukkanin nua’ukan ciwon sankara dake duniya.
Bayanin ya kara da cewa ciwon dajin mama shi ne ciwon sanakara mafi yawa wanda kuma ke haifar da mace-macen mata a duniya.
Ilbawi ya yi nuni da cewa mata masu kiba ne suka fi kamuwa da ciwon dajin na mama wanda ya fi ko wani irin ciwon daji yawa a doron kasa a halin yanzu.